Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 72:16-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar,Da ma amfanin gona yă cika tuddan,Yă yi yawa kamar itatuwan al'ul na Lebanon,Da ma birane su cika da mutane,Kamar ciyayin da suke girma a sauruka.

17. Da ma a yi ta tunawa da sunansa har abada,Da ma shahararsa ta ɗore muddin rana tana haskakawa.Da ma dukan sauran al'umma su yabi sarkin,Dukan jama'a su roƙi Allah yă sa musu albarka,Kamar yadda ya sa wa sarki albarka.

18. Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila,Wanda shi kaɗai ne yake aikata al'amuran nan masu banmamaki!

19. Ku yabi sunansa mai daraja har abada,Allah ya sa ɗaukakarsa ta cika dukan duniya!Amin! Amin!

Karanta cikakken babi Zab 72