Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 69:2-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ina nutsewa cikin laka mai zurfi,Ba kuwa ƙasa mai ƙarfi,Na tsunduma cikin ruwa mai zurfi,Raƙuman ruwa kuwa sun kusa kashe ni.

3. Na gaji da kira, ina neman taimako,Maƙogwarona yana yi mini ciwo,Idanuna duka sun gaji,Saboda ina zuba ido ga taimakonka.

4. Waɗanda suke ƙina ba daliliSun fi gashin kaina yawa,Waɗanda suke baza ƙarya suke ƙina,Suna da ƙarfi, suna kuwa so su kashe ni.Suka tilasta ni in mayar da abubuwan da ba satarsu na yi ba.

5. Zunubaina ba a ɓoye suke a gare ka ba ya Allah,Ka san irin wawancin da na yi!

6. Kada ka bar ni in jawo kunya ga waɗanda suka dogara gare ka,Ya Ubangiji Allah Mai Iko Dukka!Kada ka bar ni in jawo abin kunyaGa waɗanda suke maka sujada, ya Allah na Isra'ila!

7. Sabili da kai ne aka ci mutuncina,Kunya ta rufe ni.

8. Kamar baƙo nake ga 'yan'uwana,Haka ma ga iyalina, kamar baƙo nake.

9. Ƙaunar da nake da ita ta yin ibada a HaikalinkaTana iza ni a ciki kamar wuta,Zargin da suke yi a kanka, ya fāɗa a kaina.

Karanta cikakken babi Zab 69