Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 13:8-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Zan auka musu kamar beyar,Wadda aka ƙwace mata 'ya'ya.Zan yage ƙirjinsu, in cinye su kamar zaki,Kamar mugun naman jeji zan yayyage su.

9. “Zan hallaka ku, ya mutanen Isra'ila!Wane ne zai taimake ku?

10. Yanzu ina sarkinku da zai cece ku?Ina kuma dukan shugabanninku da za su kāre ku?Su waɗanda kuka roƙa, kun ce, ‘Ku naɗa mana sarki da shugabanni.’

11. Da fushina na naɗa muku sarki,Da hasalata kuma na tuɓe shi.

12. “An ƙunshe muguntar Ifraimu,Zunubinsa kuwa an ajiye shi a rumbu.

13. Naƙudar haihuwarsa ta zo,Amma shi wawan yaro ne,Bai fito daga mahaifar ba.

14. Zan fanshe su daga ikon lahira.Zan fanshe su daga mutuwa.Ya mutuwa, ina annobanki?Ya kabari, ina halakarka?Kan kawar da juyayi daga wurina.

15. Ko da yake Isra'ila tana bunƙasa kamar ciyayi,Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji,Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu,Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da yake cikin taskarsu.

16. Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta,Gama ta tayar wa Allahnta.Za a kashe mutanenta da takobi.Za a fyaɗa jariranta a ƙasa,A kuma tsage matanta masu ciki.”

Karanta cikakken babi Yush 13