Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yush 10:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sarakunan Samariya za su ɓace,Kamar kumfa a bisa ruwa.

8. Za a hallaka masujadan tuddai na Awen inda Isra'ila suke yin zunubi,Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma a bagadansu.Za su ce wa manyan duwatsu, “Ku rufe mu!”Su ce wa tuddai, “Ku faɗo bisa kanmu!”

9. Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra'ila!Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba.Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba?

10. Zan fāɗa wa waɗannan mutane masu zunubi, in hukunta su.Za a tattara al'ummai, su yi gāba da su,Za a hukunta su saboda yawan zunubansu.

11. “Ifraimu horarriyar karsana ce,Wadda yake jin daɗin yin sussuka,Amma na sa wa kyakkyawan wuyanta karkiya,Na sa Yahuza ta ja garmar noma,Yakubu kuwa za ta ja garmar bajiya.

12. Ku shuka wa kanku adalci,Ku girbe albarkun ƙauna,Ku yi kautun saurukanku,Gama lokacin neman Ubangiji ya yi,Domin ya zo, ya koya muku adalci.

13. Kun shuka mugunta,Kun girbe rashin adalci,Kun ci amfanin ƙarya.“Da yake dogara ga hanyarku da ɗumbun sojojinku,

14. Domin haka hayaniyar yaƙi za ta tashi a tsakanin jama'arku.Dukan kagaranku za a hallaka su.Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaƙi.An fyaɗa uwaye da 'ya'yansu a ƙasa.

15. Haka za a yi muku, ya mutanen Betel, saboda yawan muguntarku.Da asuba za a datse Sarkin Isra'ila.”

Karanta cikakken babi Yush 10