Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 4:5-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Yunusa ya fita daga birnin, ya yi wajen gabas, ya zauna. Ya yi wa kansa rumfa, ya zauna a inuwarta, yana jira ya ga abin da zai sami birnin.

6. Sai Ubangiji ya sa wata 'yar kuranga ta tsiro ta yi girma a inda Yunusa yake, don ta inuwantar da shi, ya ji daɗi. Yunusa kuwa ya yi murna da wannan 'yar kuranga ƙwarai.

7. Amma kashegari da fitowar rana, sai Allah ya sa tsutsa ta cinye 'yar kurangar har ta mutu.

8. A sa'ad da rana ta yi sama, sai Allah ya sa iskar gabas mai zafi ta huro. Yunusa ya ji kamar zai suma saboda zafin rana da take bugun kansa. Sai ya so ya mutu, ya ce, “Gara in mutu da ina zaune da rai.”

9. Amma Allah ya ce masa, “Daidai ne ka yi fushi saboda 'yar kurangar?”Yunusa ya amsa, “Hakika, daidai ne a gare ni in yi fushi, har ma in yi fushin da ya isa in mutu!”

Karanta cikakken babi Yun 4