Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yun 1:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai matuƙan jirgin suka tsorata ƙwarai, suka ce masa, “Wane irin mugun abu ne ka aikata haka?” Sun sani ya gudu ne daga wurin Ubangiji, gama ya riga ya faɗa musu.

11. Hadirin kuwa sai ƙaruwa yake ta yi. Matuƙan jirgin kuwa suka ce masa, “Me za mu yi maka domin tekun ya lafa?”

12. Yunusa ya ce, “Sai ku ɗauke ni ku jefa ni cikin tekun, sa'an nan hadirin zai lafa. Gama na sani saboda ni ne wannan hadiri mai banrazana ya auko muku.”

13. Matuƙan jirgin kuwa suka yi ta tuƙi da iyakar ƙarfinsu don su kai gaɓa, amma suka kāsa domin hadirin yana ta ƙaruwa.

14. Suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Ya Ubangiji, muna roƙonka kada ka bar mu mu halaka saboda ran mutumin nan, kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka yi abin da ya gamshe ka.”

15. Sai suka ɗauki Yunusa suka jefa shi cikin teku, nan take teku ta lafa.

16. Sai matuƙan jirgin suka ji tsoron Ubangiji ƙwarai, har suka ba da sadaka, suka kuma yi wa'adi ga Ubangiji.

17. Ubangiji kuwa ya umarci wani babban kifi ya haɗiye Yunusa. Yunusa kuwa ya yi yini uku da dare uku a cikin cikin kifin.

Karanta cikakken babi Yun 1