Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 1:7-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.

8. Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.

9. Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su.Sai suka fashe da kuka,

10. suka ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”

11. Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?

12. Sai ku koma, 'ya'yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi 'ya'ya maza,

13. za ku yi ta jira har su yi girma? Ai, ba zai yiwu ba, 'ya'yana. Ina baƙin ciki ƙwarai saboda abin da ya same ku, da yadda Ubangiji ya yi gāba da ni.”

14. Suka sāke fashewa da kuka. Sai Orfa ta yi wa surukarta, sumba, ta yi bankwana da ita, amma Rut ta manne mata.

15. Na'omi ta ce wa Rut, “Kin ga, 'yar'uwarki ta koma wurin mutanenta da wurin gumakanta, sai ki koma, ki bi 'yar'uwarki.”

Karanta cikakken babi Rut 1