Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 1:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra'ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da 'ya'yansa maza biyu.

2. Sunan mutumin, Elimelek, matarsa kuwa Na'omi, 'ya'yanta maza kuma Malon da Kiliyon. Su Efratawa ne daga Baitalami ta Yahudiya. Suka tafi Mowab suka zauna a can.

3. Elimelek, mijin Na'omi, ya rasu, aka bar Na'omi da 'ya'yansu maza biyu.

4. Sai suka auri 'yan matan Mowab, Orfa da Rut. Bayan da suka yi wajen shekara goma a can,

5. sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.

6. Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.

7. Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.

8. Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.

9. Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su.Sai suka fashe da kuka,

10. suka ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”

11. Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?

12. Sai ku koma, 'ya'yana, gama na tsufa da yawa, ba kuma zan sami miji ba. Ko da a ce ina fata in yi aure, a ce ma zan yi aure a daren nan, in haifi 'ya'ya maza,

Karanta cikakken babi Rut 1