Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 9:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, sai jama'ar Isra'ila suka taru, suna azumi, suna saye da tufafin makoki, suna zuba toka a kansu.

2. Suka ware kansu daga bāre duka, suka tsaya, suna hurta laifofinsu da na kakanninsu.

3. Sa'ad da suke tsaye a inda suke, sai suka ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu na yini, suna karanta littafin dokokin Ubangiji Allahnsu. Suka kuma ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu ɗin na yinin, suna ta hurta laifofi suna kuma yi wa Ubangiji Allahnsu sujada.

4. Sai Yeshuwa, da Bani, da Kadmiyel, da Shebaniya, da Bunni, da Sherebiya, da Bani, da Kenani suka tsaya a kan dakalin Lawiyawa, suka ta da murya da ƙarfi ga Ubangiji Allahnsu.

5. Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce,“Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku,Ku yabe shi har abada abadin.Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii,Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”

6. Sa'an nan suka yi wannan addu'a, suka ce,“Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji,Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama.Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu,Ka ba dukansu rai,Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.

7. Kai ne, ya Ubangiji Allah, ka zaɓi Abram,Ka fito da shi daga Ur ta Kaldiyawa,Ka sāke sunansa ya zama Ibrahim.

8. Ka iske shi amintacce a gare ka,Ka kuwa yi masa alkawari.Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana,Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa,Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa,Ta zama inda zuriyarsa za su zauna.Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.

9. Ka ga wahalar kakanninmu a Masar,Ka ji kukansu a Bahar Maliya.

10. Ka kuma aikata alamu da al'ajabai a kan Fir'auna,Da fadawansa duka, da mutanen ƙasarsa,Gama ka san yadda suka yi wa jama'arka danniya.Ta haka ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau.

11. Ka yi hanya ta cikin teku domin jama'arka,Ka sa su bi ta ciki a kan sandararriyar ƙasa.Ka sa waɗanda suke fafararsu suka hallaka cikin zurfin teku,Suka nutse kamar dutse.

12. Da rana ka bishe su da al'amudin girgije,Da dare ka bishe su da al'amudin wuta.

13. Ka kuma sauka a bisa Dutsen Sinai,Ka yi magana da jama'arka a can,Ka ba su ka'idodin da suka dace,Da dokoki, da kyakkyawar koyarwa.

14. Ka koya musu su kiyaye Asabar ɗinka tsattsarka,Ka kuma ba su dokokinka ta hannun Musa bawanka.

15. Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa,Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi,Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.

16. Amma kakanninmu suka yi fāriya, suka taurare,Suka ƙi yin biyayya da umarnanka.

17. Suka ƙi yin biyayya,Suka manta da dukan abin da ka yi,Suka manta da al'ajaban da ka aikata.Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba,Don su koma cikin bauta a Masar.Amma kai Allah ne mai gafartawa,Kai mai alheri ne, mai ƙauna,Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.

18. Ko sa'ad da suka yi wa kansu ɗan marakin zubi,Suka ce shi ne allahn da ya fisshe su daga Masar,Ai, sun yi maka ɓatanci, ya Ubangiji.

Karanta cikakken babi Neh 9