Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 8:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dukan jama'a suka taru wuri ɗaya a filin Ƙofar Ruwa, suka faɗa wa Ezra, magatakarda, ya kawo Attaura ta Musa wanda Ubangiji ya ba Isra'ilawa.

2. A ran ɗaya ga watan bakwai, sai Ezra, firist, ya kawo Attaura a gaban taron jama'a, mata da maza, da dukan waɗanda za su ji, su fahimta.

3. Ya karanta Littafin, yana fuskantar filin Ƙofar Ruwa, a gaban mata da maza, da waɗanda za su iya fahimta. Mutane duka kuwa suka kasa kunne ga karatun Attaura, tun da sassafe har zuwa rana tsaka.

4. Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.

5. Ezra kuwa ya buɗe Littafin a gaban jama'a duka, domin yana sama da jama'a. Sa'ad da ya buɗe Littafin, sai jama'a duka suka miƙe tsaye.

6. Sai Ezra ya yabi Ubangiji Allah Maɗaukaki.Jama'a duka suka amsa, “Amin, amin!” suna ɗaga hannuwansu. Suka sunkuyar da kansu har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada.

7. Sa'ad da jama'a suke tsaye a wurarensu, sai Lawiyawa, wato su Yeshuwa, da Bani, da Sherebiya, da Yamin, da Akkub, da Shabbetai, da Hodiya, da Ma'aseya, da Kelita, da Azariya, da Yozabad, da Hanan, da Felaya, suka fassara musu dokokin.

8. Suka karanta daga littafin dokokin Allah sosai, suka fassara musu, saboda haka jama'a suka fahimci karatun.

9. Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin.

10. Sa'an nan ya ce musu, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha ruwan inabi mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi, gama wannan rana tsattsarka ce ta Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin da Ubangiji ya ba ku shi ne ƙarfinku.”

11. Lawiyawa kuma suka bi suna rarrashin jama'a, suna cewa, “Ku yi shiru, gama wannan rana tsattsarka ce, kada ku yi baƙin ciki.”

Karanta cikakken babi Neh 8