Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 7:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Tawa ta ƙare, gama na zamakamar lokacin da aka gamatattara amfanin gona,Kamar lokacin da aka gama kalar'ya'yan inabi,Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci,Ba kuma 'ya'yan ɓaure da sukaharba wanda raina yake so.

2. Mutanen kirki sun ƙare a duniya,Ba nagarta a cikin mutane.Dukansu suna kwanto don su zub dajini.Kowa yana farautar ɗan'uwansa datarko.

3. Sun himmantu su aikata abin da yakemugu da hannuwansu.Sarki da alƙali suna nema a ba suhanci,Babban mutum kuma yana faɗar sonzuciyarsa,Da haka sukan karkatar da zance.

4. Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake,Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingenƙaya yake.Ranar da kuka sa mai tsaro,A ran nan za a aukar muku dahukunci.Yanzu ruɗewarku ta zo,

5. Kada ka dogara ga maƙwabcinka,Kada kuma ka amince da abokinka.Ka kuma kame bakinka dagamatarkaWadda take kwance tare da kai.

6. Gama ɗa yana raina mahaifi,'Ya kuma tana tayar wamahaifiyarta,Matar ɗa kuma tana gāba dasurukarta,Mutanen gidan mutum su nemaƙiyansa.

7. Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji,Zan jira ceton Allahna,Allahna zai ji ni.

8. Ya maƙiyina, kada ka yi murna akaina,Gama sa'ad da na fāɗi, zan tashikuma.Sa'ad da na zauna cikin duhu,Ubangiji zai haskaka ni.

Karanta cikakken babi Mika 7