Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 4:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, keSihiyona,Kamar mace mai naƙuda,Gama yanzu za ki fita daga cikinbirni,Ki zauna a karkara,Za ki tafi Babila, daga can za a ceceki.Daga can Ubangiji zai cece ki dagahannun maƙiyanki.

11. Yanzu al'ummai sun taru sunagāba da ke, suna cewa,“Bari a ƙazantar da ita,Bari mu zura mata ido.”

12. Amma ba su san nufin Ubangiji ba,Ba su gane shirinsa ba,Gama ya tara su ne kamardammunan da za a kaimasussuka.

13. “Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka!Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe,kofatanki kuwa tagulla,Za ki ragargaje al'ummai da yawa.”Za ki ba Ubangijin dukan duniyadukiyarsu da suka tara ta hanyarzamba,Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukanduniya.

Karanta cikakken babi Mika 4