Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Mulkin Salama na Ubangiji

1. Zai zama nan gaba, dutse indaHaikalin Ubangiji yakeZai zama shi ne mafi tsawo duka acikin duwatsu,Zai fi tuddai tsayi,Mutane kuwa za su riƙa ɗungumazuwa wurinsa.

2. Al'umman duniya za su zo, su ce,“Bari mu haura zuwa tudunUbangiji,Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila,Za mu koyi abin da yake so mu yi,Za mu yi tafiya a hanyar da yazaɓa.”Koyarwar Ubangiji daga Urushalimatake zuwa,Daga Sihiyona yake magana dajama'arsa.

3. Zai shara'anta tsakanin al'ummanduniya masu yawa,Zai sulhunta jayayyar da take tsakaninmanyan al'ummai,Za su mai da takubansu garemani,Māsunsu kuma su maishe suwuƙaƙen aske itace.Al'umma ba za ta ƙara fita zuwayaƙi ba,Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

4. Kowa zai zauna gindin kurangarinabinsa da gindin ɓaurensa.Ba wanda zai tsoratar da shi,Gama Ubangiji Mai Runduna ne yafaɗa.

5. Ko da yake al'ummai suna bingumakansu,Amma mu za mu bi UbangijiAllahnmu har abada abadin.

Kuɓutar Isra'ila daga Zaman Talala

6. Ubangiji ya ce,“A waccan rana zan tattara guragu,Da waɗanda aka kora,Da waɗanda na wahalshe su.

7. Zan sa guragu su wanzu,Korarru kuwa su zama al'umma maiƙarfi,Ni, Ubangiji, zan yi mulkinsu aSihiyona har abada.

8. “Ke kuma hasumiyar garken tumaki,tudun Sihiyona,Mulki na dā zai komo wurinki,Wato sarautar Urushalima.”

9. Yanzu, me ya sa kike kuka daƙarfi?Ba sarki a cikinki ne?Mashawarcinki ya hallaka ne,Da azaba ta auka miki kamar tamace mai naƙuda?

10. Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, keSihiyona,Kamar mace mai naƙuda,Gama yanzu za ki fita daga cikinbirni,Ki zauna a karkara,Za ki tafi Babila, daga can za a ceceki.Daga can Ubangiji zai cece ki dagahannun maƙiyanki.

11. Yanzu al'ummai sun taru sunagāba da ke, suna cewa,“Bari a ƙazantar da ita,Bari mu zura mata ido.”

12. Amma ba su san nufin Ubangiji ba,Ba su gane shirinsa ba,Gama ya tara su ne kamardammunan da za a kaimasussuka.

13. “Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka!Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe,kofatanki kuwa tagulla,Za ki ragargaje al'ummai da yawa.”Za ki ba Ubangijin dukan duniyadukiyarsu da suka tara ta hanyarzamba,Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukanduniya.