Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 4:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Zai zama nan gaba, dutse indaHaikalin Ubangiji yakeZai zama shi ne mafi tsawo duka acikin duwatsu,Zai fi tuddai tsayi,Mutane kuwa za su riƙa ɗungumazuwa wurinsa.

2. Al'umman duniya za su zo, su ce,“Bari mu haura zuwa tudunUbangiji,Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila,Za mu koyi abin da yake so mu yi,Za mu yi tafiya a hanyar da yazaɓa.”Koyarwar Ubangiji daga Urushalimatake zuwa,Daga Sihiyona yake magana dajama'arsa.

3. Zai shara'anta tsakanin al'ummanduniya masu yawa,Zai sulhunta jayayyar da take tsakaninmanyan al'ummai,Za su mai da takubansu garemani,Māsunsu kuma su maishe suwuƙaƙen aske itace.Al'umma ba za ta ƙara fita zuwayaƙi ba,Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

Karanta cikakken babi Mika 4