Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 2:10-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?

11. Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra'ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.

12. Ubangiji zai lalatar da dukan wanda ya aikata wannan, wato wanda ya farka da wanda ya amsa, ko wanda yake kawo hadayu ga Ubangiji Mai Runduna.

13. Ga kuma abin da kuke yi. Kuna cika bagaden Ubangiji da hawaye, da kuka, da kururuwa domin ba zai ƙara karɓar hadayun da kuke kawo masa ba.

14. Kuna tambaya cewa, “Me ya sa ba ya karɓar hadayunmu?” Ai, domin ya sani ka keta alkawarin da ka yi wa matarka ta ƙuruciya ne, wadda ka ci amanarta ko da yake ita abokiyar zamanka ce, da matarka.

15. Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so 'ya'yanmu su zama 'yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.

16. “Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na ce ina ƙin kisan aure, ina ƙinsa sa'ad da waninku ya yi wa matarsa haka nan. Domin haka sai ku kula da kanku kada ku keta alkawari, mutum ya zama mai aminci ga matarsa.”

17. Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”

Karanta cikakken babi Mal 2