Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 1:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Yadda kuka yi ke nan. Kun miƙa haramtacciyar hadaya ta abinci a kan bagadena, sa'an nan kuna cewa, ‘Ta ƙaƙa muka raina ka?’ To, zan faɗa muku, don kun ƙazantar da bagadena.

8. Sa'ad da kuka kawo makauniyar dabba don ku miƙa mini hadaya, kuna tsammani wannan daidai ne? Ko kuwa sa'ad da kuka kawo gurguwar dabba ko marar lafiya wannan daidai ne? Ku ba mai mulkinku irin wannan ku gani. Zai yi murna? Ko za ku sami tagomashi, a wurinsa? Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”

9. To, firistoci ku gwada, ku roƙi Allah domin ya yi mana alheri. Ai, ba zai amsa addu'arku ba, wannan kuwa laifinku ne. Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.

10. “Da ma wani daga cikinku ya rufe ƙofofin Haikali don kada ku shiga, ku hura wuta marar amfani a bisa bagadena! Ban ji daɗinku ba. Ba zan karɓi hadayun da kuke kawo mini ba,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

11. “Mutane daga kowaɗanne sassa na duniya za su girmama ni. Ko'ina za su ƙona mini halattacciyar hadaya, gama dukansu za su girmama ni,” in ji Ubangiji Mai Runduna.

Karanta cikakken babi Mal 1