Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mal 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan shi ne jawabin da Ubangiji ya ba Malakai ya faɗa wa jama'ar Isra'ila.

2. Ubangiji ya ce, “Ina ƙaunarku.”Amma ku kuka amsa kuka ce, “Ta yaya kake ƙaunarmu?”Ubangiji ya amsa, ya ce, “Ashe, Isuwa da Yakubu ba 'yan'uwan juna ba ne? Amma zuriyar Yakubu nake ƙauna.

3. Na ƙi Isuwa da zuriyarsa, na hallaka ƙasarsa ta kan tudu, wurin zamansa kuwa na ba namomin jeji.”

4. Edomawa, wato zuriyar Isuwa, sun ce, “An rurrushe garuruwanmu, amma za su sāke gina su.”Sa'an nan Ubangiji zai amsa, ya ce, “To, su gina mana, ai, zan sāke rurrushe su. Mutane za su ce da ƙasarsu, ‘Ƙasar mugaye, da al'ummar da Ubangiji yake fushi da ita har abada.’ ”

5. “Da idanunku za ku ga wannan, za ku kuwa ce, Allah mai girma ne yake a ƙasar da ba ta Isra'ila ba ce!”

Karanta cikakken babi Mal 1