Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 9:23-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.

24. Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne.

25. “Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku.

26. Na roƙi Ubangiji, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah, kada ka hallaka jama'arka, abar gādonka wadda ka fanshe ta ta wurin girmanka, waɗanda kuma ka fito da su daga Masar da ikon dantsenka.

27. Ka tuna da bayinka, su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, kada ka kula da taurinkan jama'ar nan, ko muguntarsu, ko zunubansu

28. Don kada mutanen ƙasar da ka fito da mu su ce, “Ai, saboda Ubangiji ya kāsa ya kai su ƙasar da ya alkawarta musu, saboda kuma ba ya ƙaunarsu, shi ya sa ya fito da su don ya kashe su a jeji.”

29. Amma su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fito da su da ikonka mai girma da dantsenka mai iko.’ ”

Karanta cikakken babi M. Sh 9