Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 9:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ku ji, ya Isra'ilawa, yau kuna kan haye Kogin Urdun, don ku kori al'ummai waɗanda suka fi ku yawa, sun kuwa fi ku ƙarfi. Suna da manyan birane masu dogon garu.

2. Mutane ne ƙarfafa, dogaye, zuriyar Anakawa waɗanda kuka riga kuka ji labarinsu. Ai, kun ji akan ce, ‘Wane ne zai iya tsayayya da 'ya'yan Anak?’

3. Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.

4. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kore su daga gabanku, kada ku ce a ranku, ‘Ai, saboda adalcinmu ne Ubangiji ya kawo mu mu mallaki ƙasar nan.’ Gama saboda muguntar al'umman nan ne Ubangiji ya kore su a gabanku.

5. Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.

6. Sai ku sani fa, ba saboda adalcinku ne Ubangiji Allahnku yake ba ku kyakkyawar ƙasan nan don ku mallake ta ba, gama ku jama'a ce mai taurinkai.”

7. “Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji.

8. A Horeb kuka tsokani Ubangiji, Ubangiji kuwa ya yi fushi, har yana so ya hallaka ku.

Karanta cikakken babi M. Sh 9