Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 5:14-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Amma rana ta bakwai ranar hutu ce ta Ubangiji Allahnka. A cikinta ba za ka yi kowane irin aiki ba, kai da ɗanka, da baranka, da baranyarka, da sanka, da jakinka, da kowace dabbar da kake da ita, da baƙon da yake zaune tare da kai, don barorinka mata da maza su ma su huta kamarka.

15. Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.

16. “ ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka domin ka yi tsawon rai, ka sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

17. “ ‘Kada ka yi kisankai.

18. “ ‘Kada ka yi zina.

19. “ ‘Kada ka yi sata.

20. “ ‘Kada ka yi shaidar zur a kan maƙwabcinka.

21. “ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’

22. “Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”

23. “Sa'ad da kuka ji murya tana fitowa daga duhu, harshen wuta kuma tana ci a bisa dutse, sai shugabannin kabilanku da dattawanku suka zo wurina,

24. suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu.

25. Don me za mu mutu yanzu? Gama wannan babbar wuta za ta cinye mu. Idan muka ci gaba da jin muryar Ubangiji Allahnmu, za mu mutu.

26. Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?

27. Kai, ka matsa kusa, ka ji dukan abin da Ubangiji Allahnmu zai faɗa, sa'an nan ka mayar mana da dukan abin da Ubangiji Allahnmu ya faɗa maka. Za mu ji, mu kuma aikata.’

28. “Ubangiji kuwa ya ji maganarku wadda kuka yi mini, sai ya ce, ‘Na ji maganar da jama'an nan suka yi maka, abin da suka faɗa daidai ne.

Karanta cikakken babi M. Sh 5