Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 28:26-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Gawawwakinku za su zama abinci ga dukan tsuntsayen sama, da namomin duniya. Ba wanda zai kore su.

27. Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba.

28. Ubangiji kuma zai buge ku da ciwon hauka, da makanta, da rikicewar hankali.

29. Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.

30. “Za ku yi tashin yarinya, wani ne zai kwana da ita. Za ku gina gida, wani ne zai zauna a ciki. Za ku dasa inabinku, wani ne zai girbe amfanin.

31. Za a yanka sanku a idonku, amma ba za ku ci ba. Za a ƙwace jakinku ƙiri ƙiri a idonku, ba za a mayar muku da shi ba. Za a ba magabtanku tumakinku, ba wanda zai cece ku.

32. A idonku za a ba da 'ya'yanku mata da maza ga wata al'umma dabam, za ku yi ta jin kewarsu, amma a banza, gama ba ku da ikon yin kome.

33. Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum.

34. Abubuwan da idanunku za su gani za su sa ku zama mahaukata.

35. Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.

36. “Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.

37. Za ku zama abin ƙi, da abin karin magana, da abin habaici a cikin dukan mutane inda Ubangiji zai kora ku.

38. “Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye.

39. Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi.

40. Za ku sami itatuwan zaitun ko'ina cikin ƙasarku, amma ba za ku sami man da za ku shafa ba, gama 'ya'yan za su kakkaɓe.

Karanta cikakken babi M. Sh 28