Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 26:15-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ka duba ƙasa daga Sama, daga wurin zamanka mai tsarki, ka sa wa jama'arka, Isra'ila, albarka duk da ƙasar da ka ba mu, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda ka rantse wa kakanninmu.’ ”

16. “Yau Ubangiji Allahnku yana umartarku ku kiyaye waɗannan dokoki da farillai. Sai ku lura ku aikata su da dukan zuciyarku da dukan ranku.

17. Yau kun shaida, cewa Ubangiji shi ne Allahnku, za ku yi tafiya cikin tafarkunsa, za ku kiyaye dokokinsa, da umarnansa, da farillansa, za ku kuma yi masa biyayya.

18. Yau kuma Ubangiji ya shaida, cewa ku ne jama'arsa ta musamman, kamar yadda ya alkawarta muku. Ku kuwa za ku kiyaye dukan umarnansa.

19. Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”

Karanta cikakken babi M. Sh 26