Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 25:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, ‘Ba na so in aure ta,’

9. sai matar ɗan'uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan'uwansa.’

10. Za a kira sunan gidansa cikin Isra'ila, ‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.’ ”

11. “Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta,

12. sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi.

13. “Kada ku riƙe ma'aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami.

14. Kada kuma ku ajiye mudu iri biyu a gidanku, wato babba da ƙarami.

15. Sai ku kasance da ma'aunin nauyi da mudu masu kyau don ku daɗe a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

16. Gama duk wanda yake aikata irin waɗannan abubuwa, da dukan marasa gaskiya, abin ƙyama ne su ga Ubangiji Allahnku.”

17. “Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar.

18. Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.

19. Domin haka sa'ad da Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa daga dukan magabtanku da suke kewaye da ku a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka, abar gādo, to, sai ku shafe Amalekawa daga duniya, don kada a ƙara tunawa da su. Kada fa ku manta.”

Karanta cikakken babi M. Sh 25