Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 24:3-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. idan shi kuma ya ƙi ta, ya ba ta takardar saki a hannunta, ya sallame ta daga gidansa, ko kuma idan ya mutu ne,

4. to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.

5. “Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”

6. “Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne.

7. “Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba'isra'ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.

Karanta cikakken babi M. Sh 24