Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 14:18-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.

19. “Dukan 'yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su.

20. Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.

21. “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku.“Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”

22. “Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara.

23. Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.

24. Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa'ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka,

25. to, sai ku sayar da zakar, ku tafi da kuɗin wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa,

Karanta cikakken babi M. Sh 14