Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 9:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Na daɗe ina tunani ƙwarai a kan wannan abu duka, yadda Allah yake sarrafa ayyukan masu hikima da na adalai, har da ƙaunarsu da ƙiyayyarsu. Ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba.

2. Ba wani bambanci. Makoma ɗaya ce, ta adali da ta mugu, da ta mutumin kirki da ta marar kirki, da ta tsattsarka da ta marar tsarki, da ta masu yin sujada da ta marasa yi. Mutumin kirki bai fi mai zunubi ba. Wanda ya yi rantsuwa bai fi wanda bai yi ba.

3. Duk makomarsu ɗaya ce, wannan ita ce ɓarnar da take faruwa a duniya. Muddin mutane suna da rai tunaninsu cike yake da mugunta da rashin hankali. Bayan haka sukan mutu.

4. Amma dukan wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki.

5. Hakika rayayyu sun san za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da wani sauran lada nan gaba, an manta da su ke nan sam.

6. Ƙaunarsu, da ƙiyayyarsu, da kishinsu sun mutu tare da su. Ba za su ƙara yin wani abu da ake yi a duniya ba.

7. Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.

8. Ka yi farin ciki da fara'a kullum.

9. Ka yi nishaɗi da matar da kake ƙauna, dukan kwanakin ranka na banza waɗanda Allah ya ba ka a wannan duniya, ka more kowace rana, wannan ne kaɗai rabonka na wahalar aikinka a duniya.

Karanta cikakken babi M. Had 9