Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 2:4-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Na kammala manyan abubuwa. Na gina wa kaina gidaje, na yi gonakin inabi.

5. Na kuma yi wa kaina lambuna da gonakin itatuwa, ba irin itatuwa masu 'ya'ya da ba su a ciki.

6. Na yi tafkuna na yi wa itatuwana banruwa.

7. Na sayo bayi mata da maza, an kuma haifa mini cucanawa a gidana. Ina kuma da manyan garkunan shanu, da na tumaki, da na awaki fiye da dukan wanda ya taɓa zama a Urushalima.

8. Na tara wa kaina azurfa, da zinariya, daga baitulmalin ƙasashen da nake mulki. Mawaƙa mata da maza suna raira mini waƙa, ina da dukan irin matan da kowane namiji zai so.

9. I, na ƙasaita fiye da dukan waɗanda suka riga ni zama a Urushalima. Hikimata kuma ba ta taɓa rabuwa da ni ba.

10. Duk abin da nake so, na samu, ban taɓa hana wa kaina kowane irin nishaɗin da nake so ba. Ina fariya da kowane irin abin da na aikata. Wannan shi ne ladana na dukan aikina.

11. Na yi tunani a kan dukan abin da na aikata, da irin wahalar da na sha lokacin da nake yin aikin, sai na gane ba shi da wata ma'ana, na zama kamar mai harbin iska, ba shi da wani amfani.

12. Bayan wannan duka, abin da sarki zai iya yi kaɗai, shi ne abin da sarakunan da suka riga shi suka yi.Sai na fara tunani a kan abin da ake nufi da hikima, ko rashin kula, ko wauta.

13. To, na sani hikima ta fi wauta, kamar yadda haske ya fi duhu.

14. Mai hikima ya san inda ya nufa, amma wawa ba zai iya sani ba. Na kuma sani makomarsu guda ce.

Karanta cikakken babi M. Had 2