Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:29-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Da ma a ce nake shugabancin mutanen nan, da sai in hamɓare Abimelek!” Sai ya ce wa Abimelek, “Ka tara yawan rundunarka ka fito.”

30. Zebul, shugaban birnin ya ji maganganun Ga'al, ɗan Ebed, sai ya husata.

31. Ya aiki jakadu wurin Abimelek a Aruma, ya ce, “Ga fa Ga'al, ɗan Ebed, da 'yan'uwansa sun zo Shekem, suna kutta garin ya tayar maka.

32. Yanzu sai ka tashi, ka zo da dare tare da mutanen da suke tare da kai, ku yi kwanto a cikin saura.

33. Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”

34. Abimelek da mutanen da suke tare da shi kuwa suka tashi da dare suke yi wa Shekem kwanto da ƙungiya huɗu.

35. Ga'al, ɗan Ebed, kuwa ya fita zuwa ƙofar garin daidai lokacin da Abimelek da mutanensa suka tashi daga wurin kwantonsu.

36. Sa'ad da Ga'al ya ga mutanen, ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna zuwa daga kan duwatsu.”Sai Zebul ya ce masa, “Ai, inuwar duwatsu ce kake gani kamar mutane.”

37. Ga'al kuma ya ƙara yin magana, ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa kan hanya, ga kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen oak na masu duba.”

Karanta cikakken babi L. Mah 9