Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 20:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Dukan jama'a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa.

9. Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi.

10. Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.”

11. Saboda haka dukan mutanen Isra'ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.

12. Kabilar Isra'ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?

13. Yanzu sai ku ba da mutanen nan 'yan iska da take cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra'ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar 'yan'uwansu, Isra'ilawa ba.

14. Mutanen Biliyaminu kuwa suka fita daga Gibeya gaba ɗaya domin su yi yaƙi da jama'ar Isra'ila.

15. A ran nan mutanen Biliyaminu suka tattaru daga garuruwansu, mutum dubu ashirin da shida (26,000). Banda waɗannan, sai da mazaunan Gibeya suka tara zaɓaɓɓun mutane ɗari bakwai.

16. Daga cikin waɗannan duka akwai zaɓaɓɓun mutane bakwai, bahagwai. Kowannensu yana iya ya baraci gashi guda da majajjawa ba kuskure.

17. Isra'ilawa kuwa banda kabilar Biliyaminu, suka tara mayaƙa dubu ɗari huɗu (400,000) horarru.

18. Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?”Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”

19. Sa'an nan Isra'ilawa suka tashi da safe suka kafa sansani kusa da Gibeya.

Karanta cikakken babi L. Mah 20