Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 20:37-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Sai 'yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin.

38. Alamar da mayaƙan Isra'ila da na 'yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin.

39. Idan mutanen Isra'ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra'ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.”

40. Amma sa'ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama.

41. Da mutanen Isra'ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu.

42. Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin 'yan kwanto da sauran sojojin Isra'ilawa.

43. Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas.

44. Aka kashe jarumawan mutanen Biliyaminu mutum dubu goma sha takwas (18,000).

45. Sauran suka juya, suka gudu, suka nufi wajen hamada zuwa Dutsen Rimmon. A kan hanyoyi, aka kashe musu mutum dubu biyar. Aka kuma runtumi sauran da suka ragu har zuwa Gidom inda suka kashe mutum dubu biyu.

46. Mutanen Biliyaminu da aka kashe a ran nan dubu ashirin da biyar (25,000) ne. Dukansu kuwa jarumawa ne.

47. Amma mutum ɗari shida suka juya, suka gudu suka nufi hamada zuwa Dutsen Rimmon inda suka zauna har wata hu:du.

48. Mutanen Isra'ila kuma suka komo, suka fāɗa wa sauran mutanen Biliyaminu. Suka karkashe su, mutane, da dabbobi, da dukan abin da suka iske. Suka ƙone garuruwan wannan yankin ƙasa.

Karanta cikakken babi L. Mah 20