Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 10:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da uku, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a Shamir.

3. Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da biyu.

4. Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir.

5. Yayir ya rasu aka binne shi a Kamon.

6. Isra'ilawa suka sāke yi wa Ubangiji zunubi. Suka yi sujada ga Ba'al da Ashtarot, allolin Suriyawa, da na Sidon, da na Mowab, da na Ammonawa, da na Filistiyawa. Suka bar bin Ubangiji, suka daina yi masa sujada.

7. Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa.

8. Suka murƙushe Isra'ilawa, suka matsa musu. Har shekara goma sha takwas suka yi ta matsa dukan Isra'ilawan da suke a hayin Urdun daga gabas, a cikin Gileyad, inda Amoriyawa suke zaune.

Karanta cikakken babi L. Mah 10