Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 10:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Amma Isra'ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mun yi zunubi, ka yi mana duk irin abin da ka ga dama, amma in ka yarda ka cece mu yau.”

16. Sa'an nan suka zubar da gumakan da suke wurinsu, suka yi wa Ubangiji sujada. Shi kuwa ya damu saboda azabar da Isra'ilawa suke sha.

17. Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra'ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa.

18. Shugabanni da mutanen Gileyad suka ce wa junansu. “Wa zai fara yaĆ™i da Ammonawa? Shi zai zama shugaban duk wanda yake Gileyad.”

Karanta cikakken babi L. Mah 10