Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 9:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. ya faɗa wa Isra'ilawa ya ce, “Idan wani mutum na cikinku, ko na cikin zuriyarku, ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji.

11. Za su kiyaye shi da maraice a watan biyu yana da kwana goma sha huɗu. Za su ci shi da abinci marar yisti da ganyaye masu ɗaci.

12. Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa.

13. Amma mutumin da yake da tsarki, bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi kiyaye Idin Ƙetarewa, sai a raba wannan mutum da jama'arsa, gama bai miƙa hadayar Ubangiji a ƙayyadadden lokacin yinta ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.

14. “Idan baƙo yana zaune a wurinku, shi ma sai ya kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji bisa ga umarnai da ka'idodi na Idin Ƙetarewa. Ka'ida ɗaya ce ga baƙo da ɗan gari.”

15-16. A ranar da aka kafa alfarwa ta sujada, sai girgije ya sauko ya rufe ta. Da maraice kuwa girgijen yana kamar wuta.

17. A duk lokacin da aka gusar da girgijen, sai Isra'ilawa su kama hanya. A inda girgijen ya tsaya, nan kuma Isra'ilawa za su kafa zango.

18. Da umarnin Ubangiji Isra'ilawa suke tashi, da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana bisa alfarwar, sukan yi ta zamansu a zangon.

19. Ko da girgije ya daɗe a bisa alfarwar Isra'ilawa ba sukan tashi ba, sukan bi umarnin Ubangiji.

20. Wani lokaci girgijen yakan yi 'yan kwanaki ne kawai bisa alfarwar. Tashinsu da zamansu sun danganta ga umarnin Ubangiji.

21. Wani lokaci girgijen yakan zauna a bisa alfarwar daga maraice zuwa safiya ne kawai, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi. Amma idan girgijen ya yini, ya kwana, sa'an nan ya tashi, su kuma sai su tashi.

22. Ko kwana biyu ne girgijen ya yi, yana zaune a bisa alfarwar ko wata guda, ko fi, sai Isra'ilawa su yi ta zamansu a zangon, ba za su tashi ba. Amma in ya tashi, sai su kuma su tashi.

23. Da umarnin Ubangiji suke sauka, da umarninsa kuma suke tashi, suna bin faɗarsa, yadda ya umarci Musa.

Karanta cikakken babi L. Kid 9