Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 9:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Ubangiji ya yi wa Musa magana a jejin Sinai a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar, ya ce,

2. “Sai Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa.

3. A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.”

4. Musa kuwa ya faɗa wa Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa.

5. Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.

6. Akwai waɗansu mutane da suka ƙazantu ta wurin taɓa gawar wani mutum,don haka ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a ranar ba. Sai suka zo wurin Musa da Haruna a ranar,

7. suka ce masa, “Ai, mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa. Me ya sa aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran 'yan'uwanmu a ƙayyadadden lokacin yinta?”

8. Sai Musa ya ce musu, “Dakata, har na ji abin da Ubangiji zai umarta a kanku.”

9. Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa

10. ya faɗa wa Isra'ilawa ya ce, “Idan wani mutum na cikinku, ko na cikin zuriyarku, ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Idin Ƙetarewa ga Ubangiji.

11. Za su kiyaye shi da maraice a watan biyu yana da kwana goma sha huɗu. Za su ci shi da abinci marar yisti da ganyaye masu ɗaci.

12. Kada su bar kome daga cikinsa ya kai gobe, kada kuwa a fasa ƙashinsa, sai su yi shi bisa ga dukan umarnin Idin Ƙetarewa.

13. Amma mutumin da yake da tsarki, bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi kiyaye Idin Ƙetarewa, sai a raba wannan mutum da jama'arsa, gama bai miƙa hadayar Ubangiji a ƙayyadadden lokacin yinta ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.

Karanta cikakken babi L. Kid 9