Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 28:9-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. A rana Asabar kuwa za a miƙa 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da mudu biyu na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai, domin yin hadaya ta gari tare da hadayarsa ta sha.

10. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha.

11. A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma 'yan raguna bakwai bana daya daya; marasa lahani,

12. hadaya ta gari kuma, a kwaɓa gari humushi uku na garwa da man zaitun don kowane bijimi, da gari humushi biyu na garwa don rago,

13. da kuma gari humushin garwa don ɗan rago. Waɗannan su ne hadayu na abinci na ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

14. Hadaya ta sha kuwa za ta zama rabin moɗa na ruwan inabi don kowane bijimi, sulusin moɗa kuma don kowane rago, rubu'in moɗa don kowane ɗan rago. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane wata na shekara.

15. A kuma miƙa bunsuru ɗaya na yin hadaya don zunubi ga Ubangiji tare da hadaya ta ƙonawa, da hadayarta ta sha.

16. Za a yi Idin Ƙetarewa ga Ubangiji a rana ta goma sha huɗu ga watan fari.

17. Kashegari kuwa za a fara idin kwana bakwai. A kwanakin nan, sai a riƙa cin abinci marar yisti.

18. Za ku yi tsarkakakken taro a ranar fari ta idin, ba za a yi aiki ba.

19. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimai biyu, da rago ɗaya, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya ga Ubangiji. Dukansu su zama marasa lahani.

20. Za a kuma miƙa hadaya ta gari tare da dabbobin, da lallausan gari wanda aka kwaɓa da man zaitun, gari humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gari humushi biyu tare da kowane rago,

21. gari humushi ɗaya tare da kowane ɗan rago.

Karanta cikakken babi L. Kid 28