Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 28:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Waɗannan su ne hadayu na abinci da za a miƙa wa Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta kowace rana, raguna biyu 'yan bana ɗaya ɗaya marasa lahani.

4. A miƙa ɗan rago ɗaya da safe, ɗaya kuma da maraice,

5. da kuma mudun lallausan gari, kwaɓaɓɓe da man zaitun mafi kyau har rubu'in moɗa.

6. Hadaya ce ta ƙonawa kullum, wadda aka kafa a Dutsen Sinai, don daɗin ƙanshi, hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji.

7. Hadaya ta sha za ta zama rubu'in moɗa na ruwan inabi domin kowane ɗan rago. Za a kwarara hadaya ta sha mai gafi ga Ubangiji a bagade.

8. Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice, tare da hadaya ta gari kamar ta safe, da hadayarsa ta sha. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

9. A rana Asabar kuwa za a miƙa 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da mudu biyu na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai, domin yin hadaya ta gari tare da hadayarsa ta sha.

Karanta cikakken babi L. Kid 28