Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 20:1-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai dukan taron jama'ar Isra'ilawa suka zo jejin Zin a watan fari, suka sauka a Kadesh. A nan ne Maryamu ta rasu, a nan kuma aka binne ta.

2. Da jama'a suka rasa ruwa, sai suka taru suka tayar wa Musa da Haruna.

3. Suka ce wa Musa, “Da ma mun mutu kamar yadda 'yan'uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji.

4. Don me ka fito da taron jama'ar Ubangiji zuwa cikin wannan jeji don mu mutu a nan, mu da dabbobinmu?

5. Don me kuma ka sa muka fito daga masar, ka kawo mu a wannan mugun wuri inda babu hatsi, ko ɓaure, ko inabi, ko rumman, ko ruwan da za a sha ma?”

6. Sai Musa da Haruna suka bar taron jama'a, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada, suka fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana a gare su.

7. Ubangiji ya ce wa Musa,

8. “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”

9. Musa kuwa ya ɗauki sanda daga gaban Ubangiji kamar yadda ya umarce shi.

10. Sai Musa da Haruna suka sa jama'a su taru a gaban dutsen, sa'an nan Musa ya ce musu, “Ku kasa kunne, ku 'yan tawaye, za mu fito muku da ruwa daga cikin dutsen nan?”

11. Musa kuwa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa, sai ruwa mai yawa ya yi ta kwararowa. Taron jama'a tare da garkunansu suka sha.

12. Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra'ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama'ar nan a ƙasar da na ba su ba.”

13. Wannan ya faru ne a Meriba inda mutanen Isra'ila suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda shi kuma ya nuna musu shi mai tsarki ne.

14. Sai Musa ya aika manzanni daga Kadesh zuwa wurin Sarkin Edom, su ce masa, “In ji ɗan'uwanka, Isra'ila, ka dai san dukan wahalar da ta same mu,

15. yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.

Karanta cikakken babi L. Kid 20