Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 16:32-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. ta haɗiye su tare da iyalansu, da dukan mutanen Kora, da dukan mallakarsu.

33. Haka fa, su da dukan abin da yake nasu suka gangara zuwa lahira da rai.

34. Sai Isra'ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu,kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.”

35. Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.

36. Ubangiji ya ce wa Musa,

37. “Ka faɗa wa Ele'azara, ɗan Haruna firist, ya kawar da farantan ƙona turare daga wurin da wutar ta cinye, ka watsar da gawayin daga farantan a wani wuri gama farantan tsarkakakku ne.

38. Waɗannan farantan ƙona turaren sun zama tsarkakakku sa'ad da aka miƙa su a bagaden Ubangiji. Sai ka ɗauki farantan mutanen da suka yi zunubin da ya jawo, musu mutuwa, ka ƙera murfin bagade da su, gama an miƙa su a gaban Ubangiji, ta haka za su zama gargaɗi ga jama'ar Isra'ila.”

39. Sai Ele'azara, firist, ya ɗauki farantan tagullar waɗanda mutanen da aka hallaka suka kawo. Aka ƙera murfin bagade da su.

40. Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.

41. Kashegari dukan taron Isra'ilawa suka yi gunaguni a kan Musa da Haruna, suna cewa, “Ku ne sanadin mutuwar jama'ar Ubangiji.”

42. Da taron jama'ar suka haɗa kai gāba da Musa da Haruna, sai suka fuskanci alfarwa ta sujada. Ga girgije yana rufe da alfarwar, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana.

Karanta cikakken babi L. Kid 16