Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 14:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sa'an nan Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki a gaban dukan taron jama'ar Isra'ilawa.

6. Sai Joshuwa, ɗan Nun, da Kalibu, ɗan Yefunne waɗanda suke tare da masu leƙo asirin ƙasar, suka yayyage tufafinsu.

7. Suka ce wa dukan taron jama'ar Isra'ilawa, “Ƙasar da muka ratsa ta don mu leƙi asirinta, ƙasa ce mai kyau ƙwarai da gaske.

8. Idan Ubangiji yana jin daɗinmu zai kai mu a wannan ƙasa da take cike da yalwar abinci, ya ba mu ita.

9. Sai dai kada ku tayar wa Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasar. Za mu ci su ba wuya, Ubangiji kuma zai lalatar da gumakansu da suke kāre su. Ubangiji kuwa yana tare da mu, kada ku ji tsoronsu.”

10. Amma taron jama'a suka ce za su jajjefe su da duwatsu. Sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana ga dukan mutanen Isra'ila daga cikin alfarwa ta sujada.

11. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Har yaushe mutanen nan za su raina ni? Har yaushe za su ƙi gaskata ni, ko da yake na aikata alamu a tsakiyarsu?

Karanta cikakken babi L. Kid 14