Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 11:23-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sai Ubangiji ya amsa wa Musa, “Ikon Ubangiji ya gaza ne? Yanzu za ka gani ko maganata gaskiya ce, ko ba gaskiya ba ce.”

24. Musa kuwa ya fita, ya faɗa wa jama'a maganar Ubangiji, ya kuma tattara dattawa saba'in daga cikin jama'ar, ya sa su tsaya kewaye da alfarwar.

25. Sa'an nan Ubangiji ya sauko cikin girgije, ya yi masa magana, ya kuma sa ruhun da yake kansa, ya zama a kan dattawan nan saba'in. Sa'ad da ruhun ya zauna a kansu sai suka yi annabci, amma daga wannan kuma ba su ƙara yi ba.

26. Akwai mutum biyu da suka ragu a zangon, sunan ɗayan Eldad, ɗayan kuwa Medad. Ruhun kuma ya zauna a kansu gama suna cikin dattawan nan da aka lasafta, amma ba su fita zuwa alfarwa ba, sai suka yi annabci a zangon.

27. Sai wani saurayi ya sheƙa a guje ya faɗa wa Musa, ya ce, “Ga Eldad da Medad suna nan suna annabci a cikin zangon.”

28. Joshuwa ɗan Nun, mai yi wa Musa barantaka, ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun, ya ce, “Ya shugabana, Musa, ka hana su.”

29. Amma Musa ya ce masa, “Kishi kake yi domina? Da ma jama'ar Ubangiji duka annabawa ne, har ma ya sa Ruhunsa a cikinsu!”

30. Sai Musa da dattawan Isra'ila suka koma zango.

31. Sai iska ta huro daga wurin Ubangiji, ta koro makware daga teku, ta bar su birjik kusa da zango, misalin nisan tafiyar yini guda ta kowace fuska. Tsayin tashinsu daga ƙasa misalin kamu biyu ne.

Karanta cikakken babi L. Kid 11