Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 9:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai Haruna ya matsa kusa da bagaden, ya yanka ɗan maraƙi na yin hadaya don zunubi saboda kansa.

9. 'Ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya tsoma yatsansa a cikin jinin, ya shafa a zankayen bagaden, ya kuma zuba jinin a gindin bagaden.

10. Amma kitsen, da ƙodojin, da kitsen da yake rufe da hanta na hadaya don zunubi, ya ƙone su a bisa bagaden kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

11. Naman da fatar kuwa ya ƙone su a bayan zangon.

12. Haruna ya yanka hadaya ta ƙonawa, 'ya'yansa maza kuma suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa a bagaden da kewayensa.

13. Suka kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa gunduwa gunduwa tare da kan, sai ya ƙone su bisa bagaden.

14. Ya kuma wanke kayan ciki, da ƙafafu, sa'an nan ya ƙone su tare da hadaya ta ƙonawa a bisa bagaden.

15. Haruna kuma ya miƙa hadayar jama'a. Ya ɗauki bunsuru na yin hadaya don zunubi jama'ar, ya yanka, ya miƙa shi hadaya don zunubi kamar yadda aka yi da na farin.

16. Ya kuma miƙa hadaya ta ƙonawa, ya yi kamar yadda aka faɗa.

17. Ya kuma kawo hadaya ta gari, ya ɗibi garin cike da tafin hannunsa, ya ƙone shi a bisa bagaden tare da hadaya ta ƙonawa ta safiya.

18. Sai kuma ya yanka bijima da rago don yin hadayun salama domin jama'ar. 'Ya'yansa maza suka miƙa masa jinin, sai ya yayyafa jinin a bisa bagaden da kewayensa.

Karanta cikakken babi L. Fir 9