Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 23:33-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Ubangiji kuma ya yi magana da Musa, ya ce ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa,

34. a rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi Idin Bukkoki kwana bakwai saboda Ubangiji.

35. Za a yi muhimmin taro na sujada a rana ta fari. Ba za su yi aiki ba.

36. A kwana bakwai ɗin za su riƙa miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. A rana ta takwas kuma sai su yi muhimmin taro na sujada, su miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Rana ce ta yin sujada, kada su yi aiki.

37. Waɗannan su ne ƙayyadaddun idodi na Ubangiji da za su riƙa yi domin sujada. Za su miƙa hadayu ga Ubangiji, wato, hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta gari, da ta sadakoki, da hadayu na sha. Za a miƙa kowace hadaya a ranarta.

38. Waɗannan idodi ƙari ne a kan lokatan sujada da aka saba, hadayun kuma ƙari ne a kan kyautan da aka saba bayarwa, kamar su hadaya don cika wa'adi, da hadaya ta yardar rai da suke bayarwa ga Ubangiji.

39. A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai, bayan da sun gama tattara amfanin gonakinsu, sai su yi idi ga Ubangiji har kwana bakwai. Rana ta fari, da rana ta takwas za su zama muhimman ranakun hutawa.

40. A ranar sai su ɗibi 'ya'yan itatuwa masu kyau, da rassan dabino, da kauraran rassan itatuwa masu ganye, da itacen wardi na rafi, sa'an nan su nuna bangirma gaban Ubangiji Allahnsu har kwana bakwai.

41. Za su yi idin nan ga Ubangiji har kwana bakwai. Wannan ka'ida ce a gare su har abada.

42. Za su zauna cikin bukkoki har kwana bakwai. Duk 'yan ƙasa waɗanda suke Isra'ilawa za su zauna cikin bukkoki.

43. Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra'ilawa su zauna cikin bukkoki, sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.

44. Haka kuwa Musa ya sanar wa mutanen Isra'ila da ƙayyadaddun idodin Ubangiji.

Karanta cikakken babi L. Fir 23