Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 19:16-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Kada ku yi ta yaɗa ƙarya game da wani. Sa'ad da wani yake cikin shari'ar kuɓutar da ransa, ku yi magana muddin dai shaidarku za ta taimake shi. Ni ne Ubangiji.

17. “Kada wani ya riƙe ɗan'uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi.

18. Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.

19. “Sai ku kiyaye dokokina. Kada ku bar dabbobinku su yi barbara da waɗansu iri dabam. Kada ku shuka iri biyu a gonakinku. Kada ku sa tufar da aka yi da ƙyalle iri biyu.

20. “Idan mutum ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda kuma wani yake tashinta, tun ba a fanshe ta ba, ko kuwa ba a 'yanta ta ba, sai a bincike, amma ba za a kashe su ba, domin ita ba 'yantacciya ba ce.

21. Amma ya kawo rago na yin hadaya don laifinsa ga Ubangiji a ƙofar alfarwa ta sujada.

22. Sai firist ya yi kafara da ragon hadaya don laifi saboda laifin mutumin a gaban Ubangiji. Za a kuwa gafarta masa zunubin da ya yi.

23. “Sa'ad da kuka shiga ƙasar, kuka dasa itatuwa iri iri masu ba da 'ya'ya na ci, 'ya'yan itatuwan za su zama ƙazantattu a gare ku har shekara uku. A cikin shekarun nan uku ba za ku ci su ba.

24. A shekara ta huɗu 'ya'yan itatuwan za su tsarkaka. Hadaya ce ta yabo ga Ubangiji.

25. Amma a shekara ta biyar, sai ku ci 'ya'yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku.

26. “Kada ku ci kowane abu da jininsa, kada kuma ku yi duba, ko sihiri.

27. Kada ku yi wa goshinku da gemunku kwakkwafe saboda matattu,

28. ko ku tsattsaga jikinku, ko kuwa ku yi wa kanku jarfa. Ni ne Ubangiji.

29. “Kada ku ƙasƙantar da 'ya'yanku mata ta wurin sa su su zama karuwan masujadai, idan kuka yi haka, za ku juya ga gumaka, ƙasar za ta cika da lalata.

30. Sai ku kiyaye lokatan sujada, ku kuma darajanta alfarwata mai tsarki. Ni ne Ubangiji.

31. “Kada ku tafi wurin masu mabiya, kada kuma ku nemi shawarar bokaye, domin kada su sa ku ku ƙazantu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

32. “Ku girmama tsofaffi ku darajanta su, gama kuna tsorona. Ni ne Ubangiji.

33. “Idan baƙo ya baƙunce ku a ƙasarku, kada ku cuce shi.

Karanta cikakken babi L. Fir 19