Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 16:17-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita.

18. Sa'an nan zai fita ya tafi wurin bagade wanda yake gaban Ubangiji don ya yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimin da na bunsurun, ya shafa wa zankayen bagaden a kewaye.

19. Zai kuma yayyafa jinin da yatsansa har sau bakwai a kan bagaden, ya tsabtace shi, ya tsarkake shi daga ƙazantar jama'ar Isra'ila.

20. A sa'ad da ya gama yin kafara don Wuri Mai Tsarki, da alfarwa ta sujada, da bagaden, sai ya miƙa bunsuru ɗin mai rai.

21. Haruna zai ɗibiya hannuwansa duka biyu a kan kan bunsurun mai rai, ya hurta muguntar Isra'ilawa duka a bisa bunsurun, da dukan laifofinsu, da dukan zunubansu. Zai ɗibiya su a kan kan bunsurun, ya kora shi cikin jeji ta hannun wanda aka shirya zai kora shi.

22. Bunsurun zai ɗauki muguntarsu duka a kansa zuwa jeji. Mutumin kuwa zai sake shi can a jeji.

23. Sa'an nan Haruna zai shiga alfarwa ta sujada, ya tuɓe tufafinsa na lilin waɗanda ya sa sa'ad da ya shiga Wuri Mafi Tsarki, ya ajiye su a nan.

24. Zai kuma yi wanka da ruwa a wuri mai tsarki, sa'an nan ya sa tufafinsa, ya je, ya miƙa hadayarsa ta ƙonawa, da hadaya ta ƙonawa don jama'a, domin ya yi kafara don kansa da jama'a.

25. Zai ƙone kitsen hadaya don zunubi a bisa bagaden.

26. Shi wanda ya kore bunsurun Azazel, sai ya wanke tufafinsa ya yi wanka da ruwa, bayan haka yana iya komawa cikin zango.

27. Bijimin da bunsurun da aka yi hadaya don zunubi da su, waɗanda aka yi kafara da jininsu a Wuri Mafi Tsarki, sai a kai su bayan zangon, a ƙone fatunsu, da namansu, da tarosonsu.

28. Shi wanda ya ƙone su, zai wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, bayan haka ya iya komawa zangon.

29. Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu.

30. Gama a wannan rana za a yi kafara dominsu, domin a tsarkake su daga dukan zunubansu, su zama tsarkakakku a gaban Ubangiji.

31. Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada.

32. Firist kuma da aka naɗa ya zama firist a madadin mahaifinsa, zai yi kafara yana saye da tufafin lilin masu tsarki.

Karanta cikakken babi L. Fir 16