Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Fir 13:31-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Amma idan firist ya duba mikin, ya ga zurfinsa bai zarce fatar ba, ba kuma baƙin gashi a ciki, sai firist ya kulle mai miki har kwana bakwai.

32. A rana ta bakwai kuma firist zai duba cutar, idan mikin bai bazu ba, babu kuma rawayan gashi a cikinsa, zurfin mikin kuwa bai zarce fatar ba,

33. zai aske kansa, amma ba zai aske mikin ba, sai firist ya sāke kulle mai mikin har waɗansu kwana bakwai.

34. A rana ta bakwai firist zai dudduba mikin, idan mikin bai bazu ba, zurfinsa kuma bai zarce fatar ba, sai firist ya hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne, sai mutumin ya wanke tufafinsa, ya tsarkaka ke nan.

35. Amma idan mikin ya bazu bayan tsarkakewarsa,

36. sai firist ya dudduba shi, idan mikin ya bazu a fatar, ba lalle ne ya nemi rawayan gashi ba, shi mutumin marar tsarki ne.

37. Amma idan a ganinsa mikin bai yaɗu ba, baƙin gashi ya tsiro ya kuma yi tsawo a wurin, mikin ya warke ke nan, mutumin ya tsarkaka, firist kuwa zai hurta, cewa, shi mutumin tsarkakakke ne.

38. Idan a fatar jikin mace ko namiji akwai fararen tabbai,

39. sai firist ya dudduba, idan tabban toka-toka ne, mawanki ne ya faso a fatar, shi tsarkakakke ne.

40. Idan gashin kan mutum ya zube, ya zama mai sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.

41. Idan gashin goshin mutum ya zube, ya yi sanƙo ke nan, amma shi tsattsarka ne.

42. Idan a sanƙon ko a gaban goshi akwai tabon cuta jaja-jaja da fari-fari, to, kuturta ce ta faso a sanƙonsa ko gaban goshinsa.

43. Firist kuwa zai dudduba shi, idan an ga kumburin jaja-jaja da fari-fari ne a sanƙon kansa, ko a gabansa kamar alamar kuturta a fata jikinsa,

44. to, kuturu ne shi, marar tsarki. Firist zai hurta, cewa, shi mutumin marar tsarki ne, cutar kuturta tana kansa.

45. Mai kuturta zai sa yagaggun tufafinsa, ya bar gashin kansa ba gyara, sa'an nan ya rufe leɓensa na sama, ya ta da murya, ya riƙa cewa, “Marar tsarki, marar tsarki.”

46. Muddin yana da cutar, zai zama marar tsarki. Zai zauna shi kaɗai a bayan zango.

47. Idan ana tsammani akwai cutar kuturta a rigar ulu ko ta lilin,

48. ko a tariyar zaren, ko a waɗari, ko a lilin, ko a ulu, ko a cikin fata, ko cikin kowane abu da aka yi da fata,

49. idan cutar ta zama kore-kore, ko jaja-jaja a rigar, ko a fatar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko a kan abin da aka yi da fata, wannan cuta kuturta ce, sai a nuna wa firist.

Karanta cikakken babi L. Fir 13