Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 30:17-29-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.

18-19. Akwai abu uku, i, har huɗu ma, waɗanda ban iya fahimtar su ba, watoyadda gaggafa take tashi a sararin sama,yadda maciji yake jan ciki a kan dutse,yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku,Sha'anin namiji da 'ya mace.

20. Ga yadda al'amarin mazinaciya yake, takan yi sha'aninta sa'an nan ta yi wanka ta ce, “Ban yi laifin kome ba!”

21-23. Akwai abu uku, i, har huɗu ma waɗanda duniya ba ta jurewa da su, watobara da ya zama sarki,wawa da ya ƙoshi da abinci,mummunar mace da ta sami miji,baiwar da ta gāji uwargijiyarta.

24-28. Akwai ƙananan abubuwa huɗu a duniya, amma suna da hikima ƙwarai, watotururuwa talikai ne marasa ƙarfi, amma duk da haka sukan tanadi abincinsu da rani,remaye ba ƙarfafa ba ne, duk da haka suna yi wa kansu gidaje a cikin duwatsu,fara ba su da sarki, amma duk da haka suna tafiya sahu-sahu.ƙadangare ma wanda ka iya kama shi a hannu, amma yana zama a cikin fādodin sarakuna.

29-31. Akwai abu uku, i, har huɗu ma da suke da kwarjini da taƙama a tafiyarsu, watoZaki wanda ya fi dukan dabbobi ƙarfi, ba ya ratse wa kowa daga cikinsu,bunsuru da zakara mai taƙama,sarkin da yake tafiya gaban jama'arsa.

Karanta cikakken babi K. Mag 30