Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

K. Mag 14:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Hikimar mata takan gina gidaje, amma wauta takan rushe su.

2. Ka yi gaskiya, za ka nuna girmamawarka ga Ubangiji, amma idan ka yi rashin gaskiya, ka nuna rashin girmamawa ke nan ga Ubangiji.

3. Kalmomin mai hikima za su kiyaye shi, amma maganganun wawa za su jawo masa hukunci.

4. Idan ba ka da shanun noma ba za ka sami hatsi mai yawa ba, amma idan kana da su za ka sami hatsi mai yawan gaske.

5. Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.

6. Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.

7. Ka nisanci wawaye, gama ba su da abin da za su koya maka.

8. Me ya sa haziƙi yake da hikima? Domin ya san abin da zai yi. Me ya sa dakiki yake wauta? Domin yana ganin kansa masani ne.

9. Idan wawaye sun yi zunubi ba sukan kula ba, amma mutanen kirki sukan nemi gafara.

10. Ɓacin ranka naka ne, murnarka kuwa ba za ka raba da wani ba.

11. Gidan mutumin kirki ba zai rushe ba bayan da an lalatar da gidan mugun mutum.

12. Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.

13. Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa'ad da murna ta tafi, ko yaushe baƙin ciki yana nan.

14. Mugu zai sami abin da ya cancance shi, mutumin kirki kuma zai sami sakayyar ayyukansa.

Karanta cikakken babi K. Mag 14