Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 7:5-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Mutanen Ai suka kashe mutum wajen talatin da shida daga cikin Isra'ilawa, suka runtume su tun daga ƙofar garin har zuwa Shebarim, suka yi ta karkashe su har zuwa gangaren. Zukatan mutanen Isra'ila kuwa suka narke, suka zama kamar ruwa.

6. Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu.

7. Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'an nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun.

8. Ya Ubangiji, me zan ce bayan da Isra'ilawa sun ba da baya ga abokan gābansu?

9. Gama Kan'aniyawa da dukan mazaunan ƙasar za su ji labari, su kewaye mu, su shafe sunanmu daga duniya, to, me za ka yi don sunanka mai girma?”

10. Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “Tashi, don me ka fāɗi rubda ciki?

11. Isra'ilawa sun yi zunubi. Sun ta da alkawarina, wanda na umarce su, gama sun ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, sun sa a kayansu, sun yi ƙarya.

12. Saboda haka Isra'ilawa ba su iya tsayawa a gaban abokan gābansu ba, sun ba da baya ga abokan gābansu, gama sun zama haramtattu don hallakarwa. Daɗai, ba zan kasance tare da ku ba, sai dai kun kawar da haramtattun abubuwa da suke cikinku.

13. Tashi, ka tsarkake jama'a, ka ce, ‘Ku tsarkake kanku domin gobe, gama Ubangiji, Allah na Isra'ila ya ce akwai haramtattun abubuwa a tsakiyarku. Ya Isra'ila, ba ku iya tsayawa a gaban abokan gābanku ba, sai kun kawar da haramtattun abubuwa daga tsakiyarku.

Karanta cikakken babi Josh 7