Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 7:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma Isra'ilawa suka ci amana, gama Akan, ɗan Karmi, ɗan Zabdi, ɗan Zera na kabilar Yahuza ya ɗiba daga cikin abubuwan da aka haramta, Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.

2. Joshuwa kuma ya aiki mutane daga Yariko zuwa Ai wadda take kusa da Betawen gabashin Betel, ya ce musu, “Ku tafi ku leƙi asirin ƙasar.” Sai mutanen suka tafi, suka leƙo asirin Ai.

3. Da suka komo wurin Joshuwa, sai suka ce masa, “Kada dukan mutane su tafi, amma a bar mutum wajen dubu biyu ko uku su tafi su bugi Ai, kada a sa dukan mutane su sha wahalar zuwa can, domin su kima ne.”

4. Sai mutum wajen dubu uku daga cikin jama'a suka tafi, amma mutanen Ai suka kore su.

5. Mutanen Ai suka kashe mutum wajen talatin da shida daga cikin Isra'ilawa, suka runtume su tun daga ƙofar garin har zuwa Shebarim, suka yi ta karkashe su har zuwa gangaren. Zukatan mutanen Isra'ila kuwa suka narke, suka zama kamar ruwa.

Karanta cikakken babi Josh 7