Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Josh 22:13-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Mutanen Isra'ila kuwa suka aiki Finehas, ɗan Ele'azara, firist, wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad.

14. Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra'ila.

15. Da suka zo wurin Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa a ƙasar Gileyad, ya ce musu,

16. “In ji dukan taron jama'ar Ubangiji, ‘Wane irin cin amana ne wannan da kuka yi wa Allah na Isra'ila har da kuka bar bin Ubangiji yau?’ Kun tayar wa Ubangiji yau da kuka gina wa kanku bagade.

17. Zunubin da aka yi a Feyor, ashe, bai ishe mu ba, har annoba ta wahalar da taron jama'ar Ubangiji? Ga shi, har yanzu ma ba mu gama tsarkakewa daga wannan zunubi ba.

18. Za ku kuma daina bin Ubangiji ne yau? Idan kuka tayar masa yau, gobe zai yi fushi da dukan jama'ar Isra'ila.

19. Idan ƙasar mallakarku ƙazantacciya ce, sai ku haye zuwa ƙasar Ubangiji inda alfarwa ta sujada take, ku sami abin mallaka a tsakaninmu, amma kada ku tayar wa Ubangiji, ku kuma tayar mana ta wurin gina wa kanku wani bagade dabam da bagaden Allahnmu.

20. Lokacin da Akan, ɗan Zera, ya yi rashin aminci cikin abubuwan da aka haramta, ai, dukan Isra'ilawa aka hukunta. Ba shi kaɗai ya hallaka don zunubinsa ba.”

21. Sai Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka amsa wa shugabannin iyalan Isra'ilawa suka ce,

22. “Allah Maɗaukaki, Allah Ubangiji ya sani, bari Isra'ilawa kuma da kansu su sani. Idan tayarwa ce, ko kuwa mun yi wa Ubangiji rashin aminci ne, to, kada ku bar mu da rai yau.

23. Idan mun bar bin Ubangiji, muka gina wa kanmu bagade don mu miƙa hadayun ƙonawa, ko kuwa hadayun gari, ko kuwa hadayun salama, to, bari Ubangiji kansa ya sāka mana.

24. Saboda gudun gaba ne muka yi haka, domin kada wata rana 'ya'yanku su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ruwanku da Ubangiji, Allah na Isra'ila.

25. Gama Ubangiji ya sa Kogin Urdun ya zama iyaka tsakaninmu da ku Ra'ubainawa da Gadawa domin haka ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’ To, da haka 'ya'yanku su hana 'ya'yanmu yi wa Ubangiji sujada.

26. Don haka muka ce, ‘Bari mu gina bagade, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba,

27. amma domin ya zama shaida tsakaninmu da ku, da tsakanin zuriyarmu da taku, don mu ci gaba da bautar Ubangiji da hadayunmu na ƙonawa, da na sadaka, da na salama.’ 'Ya'yanku kuma ba za su ce wa 'ya'yanmu, ‘Ba ku da wani rabo a cikin Ubangiji.’

28. Mun yi tunani, cewa idan wata rana aka ce mana, ko aka ce wa zuriyarmu haka, sai mu ce, ‘Ku dubi bagaden Ubangiji wanda iyayenmu suka gina, ba domin miƙa hadayu na ƙonawa, ko na sadaka ba, amma domin shaida a tsakaninmu da ku.’

29. Allah ya sawwaƙa mana mu tayar wa Ubangiji, mu bar bin Ubangiji, har mu gina wani bagade don miƙa hadayu na ƙonawa, da na gari, da na sadaka, banda bagaden Ubangiji Allahnmu, wanda yake a gaban mazauninsa.”

30. Sa'ad da Finehas, firist, da shugabannin jama'a, wato shugabannin iyalan Isra'ila, suka ji maganar da Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa suka faɗa, suka ji daɗi a rai.

31. Sa'an nan Finehas, ɗan Ele'azara, firist, ya ce wa Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin Manassawa, “Yau mun sani Ubangiji yana tare da mu domin ba ku ci amanar Ubangiji ba.”

Karanta cikakken babi Josh 22